[ Fatawa ] Menene gaskiyar Magana gameda cewa ba'ayin Sallama ga Mai cin abinci ko Mai karatun Al-Kur-Ani??

Share:

Tambaya 

Menene gaskiyar Magana gameda cewa ba'ayin Sallama ga Mai cin abinci ko Mai karatun Al-Kur-Ani??Amsa:

Alal-Haƙiƙa Sallama wani abune Mai-Ƙima dakuma daraja atsakanin 'Yan'uwa Musulmai, shiyasa Shari'a take kwaɗaitar damu cewa muriƙa yaɗa Sallama atsakaninmu, domin yawan yaɗa Sallama yana ƙara Soyayya da ƙauna atsakanin 'Yan'uwa Musulmai, kamar yadda Mαnzon Aʟʟaн(ﷺ) Yakecewa

لا تدخلوا الجنة حتي تؤمنوا، ولا تؤمنوا حتي تحابوا، أولا أدلكم علي شيء إذا فعلتموه تحاببتم؟ أفشوا السلام بينكم" (رواه مسلم)

MA'ANA:

(Annabi(ﷺ) Yace bazaku shiga Aljanna ba har-sai kunyi Imani, kuma bazakuyi Imani ba har-sai kun ƙaunaci junanku, Shin bana shiryar daku zuwaga abinda idan kun aikatashi zaisa kuriƙa son junankuba? Kuyaɗa (ku yawaita) Sallama atsakaninku.

Sannan kuma kamar yadda Shari'a ta tabbatar da cewa fāra yin Sallama Mustahabbine, amma kuma amsata Wajibine, Danhaka kenan wanda yafara yin Sallama yafi wanda ya amsata yawan lada, shiyasa Malamai sukace acikin dukkan ayyukan Ibada zaka samu cewa duk abinda yake Farillane ko Wajibi to yafi yawan lada akan wanda Yake Sunnane kokuma Mustahabbi, amma aɓangaren Sallama sai yakasance Mustahabbi yafi Farilla yawan lada,

Amma dangane da abinda yashafi hukuncin yin Sallama ga mai cin abinci ko karatu, ansamu wasu daga Cikin Malamai dasuka ware waɗansu abubuwa kamar guda (14)ko sama dahaka waɗanda suke ganin cewa Makaruhi ne ayiwa Mutum Sallama idan yakasance a ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa kamar haka

(1)-Idan Mutum yana cikin Cin-Abinci ko Shan wani Abin-Sha,

(2)-Idan Mutum yana cikin yin Zakirī kamar Hailala ko Tasbīhi kokuma karātun Al-ƙur-āni,

(3)-Idan Mutum ya Shagaltu da karanta Hadisan Mαnzon Allαh(ﷺ) sukace shima Makarūhīne ayimasa Sallama,

(4)-Idan Mutum yana cikin yin wata Lakca ko Tunātarwa,

(5)-Idan Mutum yana cikin karantarwa ko yana ɗaukan darasi kamar na Ilimin Al-ƙur-āni ko Hadisi kokuma Fiƙihu,

(6)-Idan Mutum yana cikin yin wani bincike na Ilimi to shima Makarūhīne ayimasa Sallama saboda kada a shagaltar dashi,

(7)-Idan Mutum yana cikin yin Wa'azi ga Mutane,

(8)-Idan Mutum yana cikin yin Muzākara (Mai-maita karatu) na ilimin da yaje ya koyo,

(9)-Idan Mutum yana cikin yin Ƙiran Sallah (Al'azān),

(10)-Idan Mutum yana cikin yin Sallah,

(11)-Idan Mutum yana cikin yin Alwala,

(12)-Idan Mutum yana hira da wani sukace Makarūhīne ayimasa Sallama donkada a katseshi,

(13)-Idan Mutum yana cikin biyan buƙatarsa kamar Fitsāari ko Kashi,(14)-Idan Mutum yana cikin yanayi na Yaƙi da abokan gaba,

To Saidai kuma waɗansu daga cikin Malamai sukace gabaɗayan waɗannan abubuwa da su waɗancan Malamai suka ambacesu: babu Nassi ko guda ɗaya dasuka dogara akansa wanda yake tabbatar da Maganarsu, danhaka kenan Maganar cewa Makaruhi ne batama tasoba, danhaka waɗannan abubuwa sunan a Asalinsu na halacci (Mustahabbi) domin Nassosin da sukazo sukayi Magana akan hukuncin Sallama, (عام/Ām) ne, Kuma ba'samu wani Nassi dayayi (تخصيص/Taksīs) nawaɗancan Nassosin ba, Sannan Malamai sukace wani Sahābi yāyiwa Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ) Sallama ayayin da yake Sallah, sai Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ) ya amsa masa amma ta hanyar yin ishārada hannunsa , Sai Mālamai sukace idan kuwa har za'ayiwa Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ) Sallama yana Sallah kuma bai hanaba, to

                  (مِـنْ بَـابِ أَوْلَـيٰ)

_Ayiwa Mai cin abinci dakuma Mai karatun Al-ƙur-āni Sallama, Danhaka dai Magana mafi inganci itace ya halatta suma ayimusu Sallama

No comments