[Fatawa] INA CIKIN SALLAH, SAI NA TUNA AKWAI NAJASA A HULATA?

Share:

                             ﷽
  Assalmu Alikum warahamatullah.TAMBAYA:

Aslm Mallam,mutun ne yana tsakiyar sallah ya kai raka'a ta biyu sai ya tuna kamar akwai najasa a hularsa,amma bai tabbatar ba sai ya cire hular, ya cigaba da sallah,toh ya sallar sa take?

AMSA:

Wa alaikumus salaam, wanda ya tuna da najasa a hularsa, zai iya hanzari ya cire ta ya yar, in har ya yi haka sallarsa ta yi, saboda abin da aka rawaito cewa: Annabi, Sallallahu alaihi wa sallama, wani lokaci yana sallah, sai ya cire takalminsa, daga baya sai yake bawa sahabbansa labari cewa: Jibrilu ne ya ce maşa akwai najasa a jiki, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, kuma Nawqawy ya inganta shi a Al-muhazzab 3\132, hadisin sai ya nuna ingancin sallar wanda ya yı haka, tun da ba'a rawaito Annabi, Sallallahu alaihi wa sallama, ya sako sallarsa daga farko ba.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa.

No comments