[ Fatawa ] Biyan bashin wanda ke binka bashi sai ya mutu kafin kabiya shi.

Share:

                  ﷽

Assalamu alaikum

Tambaya: Mutum ne yake binka bashi sai dagabaya bayan yarasu katuna,shin zaka iya kayimishi sadaka da kudin da niyyar ladan isa gareshi?

AMSA:Daga Lokacin da Labarin Mutuwar Wani Mutun yazo Maka, Alhalin wannan mutumin yana binka bashi, zakayi kokarin neman magadansa, domin ka basu kudinsu, Sabida a yanzu wannan kudin hakkin Su ne, tinda baya Raye, kenan yanzu wannan dukiyar ba tasa bace, ta magada ce. 

  Sai idan baka San inda Magadan wannan mutumin sake ba, to Anan ne zakayi masa sadaka da adadin wannan kudin da yake binka, domin ladan ya shiga cikin Sikelinsa a Ranar Alkiyama, idan kayi haka insha Allahu Ladan zai kai gare shi. 


Allah shine mafi sani

Almustapha suleiman kankia

No comments