[Fatawa] AZUMIN KWANA UKU A WATAN RAJAB

Share:

                        ﷽

Assalamu alaikum warahamatullah.

AZUMIN KWANA UKU A WATAN RAJAB ! !

Tambaya

Assalamu alaikum inayiwa malan fatan alkhairi, tambayata iyace :- Azumi uku na tsakiyar wata wanda ake kira " Ayyaamul beed " na watan Rajab

To ya hallata a muslunci?.

Amsa

Wa alaikum assalam,

Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi mai lamba ta: 761: Annabi s.a.w. ya cewa Abu-zarrin idan za ka yi azumi, to ka azumci ranar sha uku da ranar sha hudu da sha biyar daga kowanne wata, watan Rajab Daya ne dağa cikin watannin musulunci za'a iya azumin da ya tabbata a ragowar watanni a cikinsa, saidai kawai watan bai kebanta da Wata falala ba.

Allah ne mafi sani

Amsawa

Dr jamilu Zarewa

No comments