[Fatawa] ALAMOMIN ILIMI MAI AMFANI.

Share:

                           ﷽

ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH

ALAMOMIN ILIMI MAI AMFANI

Tambaya:

Don Allah malam ayi min bayanin alamomin ilimi mai amfani.

Amsa:

To dan'uwa akwai abubuwa da yawa da suke nuna ilimi mai amfani, ga muhimmai daga ciki:

1. AIKI DA ILIMI

Yana daga cikin alamomin ilimi mai amfani aiki da shi, domin duk ilimin da ya zama ba’a aiki da shi, to saidai ya cutar da ma’abocin shi amma ba zai amfane shi da komai ba, kamar yadda Annabi (s.aw.) ya ke cewa ( Al-Qur’ani hujja ne gare ka ko kuma akanka) Muslim ne ya rawaito, ma’ana idan ka yi aiki da shi sai ya zama hujja gareka ranar alkiyama, Allah (s.w.t.) ya shigar da kai aljanna da shi, idan kuma ba ka yi aiki da shi ba, sai ya zama hujja akanka, a fara hura wuta da kai kamar yadda Annabi (s.aw.) ya fada a hadisi

2. RASHIN YIWA MUTANE GIRMAN KAI

Girman kai kuwa ba sifa ce ta daibin ilimi ba, saboda malamai magada Annabawa ne, kuma daga cikin siffofin Annabi (s.aw.) akwai kaskantar da kai, kuma yana cewa ( Allah (s.w.t.) ya yi wahayi zuwa gare ni cewa : ku kaskantar da kai, ta yadda wani ba zai yi alfakhari ga wani ba). Muslim

Sai dai wannan ba ya nufin dalibi ya zama sakarai yadda kowa zai raina shi, ya kamata tare da haka ya zama mai mutunta kansa, mai kare girman iliminsa.

3. KYAUTATA ZATO GA MUTANE

Ana so dalibin ilimi ya zama mai kyautata zato ga mutane, idan mutane suka yi abu, ya samu hanyar da zai nema musu uzuri, to ya yi hakan, kada ya munana zato ga mutane, saidai idan mutumin ya kasance mai aiyuka ne marasa kyau, to wannan babu laifi don an munana masa zato.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jameel Zarewa

No comments