[Fatawa] BANBANCI TSAKANIN MUSALLA DA MASJID

Share:

                             ﷽

Assalamu alaikum warahamatullah.


Tambaya


Assalamu alaikum mallam don Allah akwai fifiko ko banbanci tsakanin masjid da musalla? Nagode.


Amsa


Wa'alaikumussalam Warahmatullahi  Wabarakatuhu, Musallah  Shine  dukkan wurin da'aka  kebeshi  don  yin sallah  koda ana aikata wassu  ababe acikinsa, sannan  ginannene  koba ginanneba koda  ba abada  wakafinsa domin yin sallah ba, 

Sannan  baya halasta  mutum yayi ittikafi acikinsa  kuma  babu lefi mutum idan wani abinsa yabace yayi sanarwa acikinsa haka kuma me haila ko janaba babu lefi su zauna acikinsa,  Amma masjid shine Wurin da akabada Wakafinsa domin yin sallah, shine kuma yake halasta mutum yayi ittikafi cikinsa kuma haramunne mutum yayi  cigiyar  wani abinsa da yabace acikinsa sannan  mace me jinin Al'ada ko  dukkan wani me janaba yake haramta su zauna cikinsa. 

والله أعلم.

Domin neman karin bayani zaka iya duba :


١. الشرح الممتع  الفضيىلةالشيخ صالح العثيمين،ج١٠، ص:

(٣٧١).


الفتاوى اللجنة الدائمة رقم:(١٣١٩)

26/03/2019


No comments