[[Siyasar Kano]] Kwankwaso Ya Karbi Nasiha Daga Wajen Malam Ibrahim Khalili

Share:

A yayinda siyasar Kano ta dauki zafi tsakanin wani tsagi na Malaman kungiyar Izala dake Kanon kan wasu furuci da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya Engr. Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso yayi, Lafazin da malaman ke ganin ba komai bane face Izgili ga akidarsu.


Sai dai wata majiya ta tabbatar mana da cewa tun a washe garin ranar da maganar ta fita shugaban majalisar malamai ta jihar Kano kuma tsohon mai bawa gwamna Ganduje Shawara yayi tattaki kafa da kafa har gida inda ya nusash-she da Kwankwason kan batun, kuma majiyar ta tabbatar da cewa Kwankwason yayi godiya matuka tare da amsar gyaran da Malam Khalil yayi masa.

Allah Ya Kyauta.

Almustapha Suleiman kankia

abuabdullahi.com.ng 

07035674655

No comments