Fatawa Akan Maza masu munanama Matan Aurensu

Share:

 
HUKUNCIN MIJIN DAKE MUNANA WA MATARSA :
                               ﷽

   FATAWAR MUSULUNCI
                   ﷽

Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu. Malam menene hukuncin namijin da yake wulakanta matarsa har yakai data gudu ma'ana yaji harna tsawon wata (biyar)5 amma bai waiwayeta ba ?
daga Idris Nazifi tsurutawa karamar hukumar lere local government kaduna state.
AMSA:Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Acikin Alqur'ani Allah madaukakin sarki ya wajabta wa bayinsa muminai masu aure crwa su rike da adalci da kyautatawa. Yace :
"KU ZAUNA DASU DA KYAUTATAWA".
Kuma Manzon Allah (saww) yayi ma al'ummarsa wasiyyar cewa su kyautata wa Matayensu na aure. Har acikin m hudubarsa ta ban-kwana yaym fa'di haka. Haka ma acikin wasiyyarsa ta karshe.
Duk da cewa idan ana zaune dole watarana a samu sabani, to amma shi namiji amatsayinsa na jagora shi yake da alhakin gyara matsalar cikin gidansa ba tare da wani yaji labari ba. Idan kuma har iyalinsa tayi yaji (Ta tafi gidan iyaye ko waliyyanta) to shi keda alhakin bin sawunta domin asamu daidaito. Duk da cewa ita dinma hakuri ya kamata tayi ta zauna agidan mijinta ba wai tafiya yaji ba.
Idan kuma shi mijin bai je biko ba, to ku 'yan uwanta sai ku kirashi ko ku kira waliyyansa ku zauna gaba daya domin fahimtar juna da yin sulhu. Haka Allah yayi umurni acikin Alqur'aninsa mai girma.
Manzon Allah (saww) yace "MAFIFITA ACIKINKU SUNE WADANDA SUKA FI (AIKATA) ALKHAIRI GA MATAYENSU".
Allah shi gyara tsakanin dukkan ma'auratan dake fama da matsaloli ameen

         Almustapha suleiman Idris kankia
         abuabdullah.com.nguni
          07035674655

No comments