[[Karanta Yanzu]] Hanyoyi Bakwai (7) Da Zaka Tantance Sakonnin karya a WhatsApp

Share:

[[Karanta Yanzu]] Hanyoyi Bakwai (7) Da Zaka Tantance Sakonnin karya a WhatsApp


(Yadda Ake Gane Labaran Karya a WhatsApp)


Acikin shekarar data gabata rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wata Matar Aure da kuma Group Admin na wani zauren WhatsApp saboda aikata laifin yada labaran karya a dandanlin sada zumunta na WhatsApp.


Da yawa mutane suna fadawa cikin wannan hali na yada labaran karya a WhatsApp ba tare da sun san illa da kuma cutarwar da hakan ke haifarwa ba, tuntuni dai a wasu kasashen an jima da daukan tsauraran matakai akan WhatsApp saboda irin wadannan bayanai da ke saurin yaduwa ta cikinsa.


A yanzu haka WhatsApp yana ta bada sanarwa a kafafan yada labarai kan jama’a su taimaka su bashi hadin kai su gujewa wannan dabi’a.


A wannan lokacin da muke dab da Babban Zaben 2019 na lura yadda jama’a da dama suka kasa gane abinda yakamata su yada da wanda bai kamata su yada ba, hakan yasa naga yiwuwar yin wannan rubutun wanda zanyi bayanin akan yadda zaka tantance ingancin sakon da aka turo maka, da kuma sakon da ya halatta kayi share da wanda bai halatta kayi ba, ba don komai ba sai don mu gudu tare mu kuma tsira tare.


1. Ka kula da sakon da akayo maka FORWARDING duk wani sako da aka turo maka ka duba da kyau idan kaga an rubuta FORWARDING to yana nufin wannan sakon bana wanda ya aiko maka dashi bane, daga wurin wani shima ya dauko, don haka akwai bukatar ka bukaci sanin karin haske na tabbacin wannan sakon.


2. Ka lura da sakon Audio, Video da Hotuna, yanzu zamani ne da muke ciki na cigaban kimiyya da fasaha mai zurfi wadda a turance ake kira da ÐIGITAL ERRA to ka kula da kyau ana iya hada sauti na karya, haka hoto dama shi kansa videon misali a kwanaki na arikici a jihar Plateau an kashe mutane da dama wani ya dauko wani hot ya saka cewa na wannan rikicin da ake yine, amma a karshe bincike ya gano wannan hoton ma na wani AMERICAN FILM ne to a nan kana bukatar ka tabbatar ka binciki sahihanci shin daga ina hoto yake? Wace jarida ce ta buga labarin? Kada ka manta yanzu abune mai sauki a hada wadancan abubuwan na karya.


3. Ka Lura da Links din da ake turo maka, akwai Links da dama marasa Inganci WhatsApp yana yin iya kokarinsa wajen fitar da alama akan Links marasa kyau, zaku gay a rubuta “SUSPICIOUS LINK” to kana ganin wannan kada ka shiga, duba misali a hoton dake kasa.


4. Kada kayi Forwarding na Messages saboda wani yace maka Don Allah kayi ko yayi maka wata magiya, kayi share na duk sakon da ka tabbatar da ingancinsa kadai, ka kula da duk sakon da za’a ce idan ka turawa mutane kaza zaka samu kaza, ko kuma in baka turawa mutane sako ba wani abu zai sameka.


5. Ka kula duk sakon da wani zaice maka ga wani abu ya faru a wuri kaza ko ana rigima bayan kai baka gani ba, zaku ga ana turo sako na muryar wani yana bada labarin wani tatsuniyarsa kuma nan da nan sai kaga jama’a suna ta yadawa wanda in an kamasu bazasu iya kawowa ba.


6. Idan aka turo maka sako baka aminta dashi ba to kaje online kayi searching in an bada sunan jarida ko sunan mutum ka bincika sahihancinsa.


7. Idan kana fargaba ko kaga an turo maka wani sako mai hatsari to gaggauta sanarwa ‘yan uwanka da jami’an tsaro mafi kusa da kai.


NOTE: Duk wanda ka tabbatar ya turo maka labarin karya to ka tabbatar ka yanka masa WARNING!! cewa kada ya kuskura ya kara turo maka wannan sakon.


Nagode sosai da ka tsaya ka karanta wannan cikakken bayanin.


Basheer Sharfadi

Social Media Strategists

Email: info@sharfadi.com

Phone: 09035830253

17-02-2019

#WeSayNotoFakeNews #Peace4Arewa #WeAre4Peace

No comments