[Garabasa] Horaswa kyauta akan sana'a a yanar gizo

Share:

Assalamu alaikum

*Ku Matso Kusa*


Na lura da wasu Fans dina na Facebook da WhatsApp suna saka hotunan tallan kayayyakin da suke siyarwa a saboda haka mun shirya zamu dauki mako guda muna koyar dasu abubuwa kamar haka:


1. Yadda mutum zai gyara hotunan kayansa ko ya rubuta lambar wayarsa da sunan kamfaninsa a jiki.

2. Yadda zai tsara talla na Video.

3. Yadda ake yin rubutun talla a social media.

4. Yadda zai tsara karbar kudi online payment

5. Yadda zaiyi register cikin sauki da hukuma.


Mutane 250 zamu koyar daga ranar Asabar 16 zuwa Jumu'a 22 ga watan March 2019.


Online za'ayi shi kuma kyauta ne.


Zamu fitar da portal na register kafin lokacin.


Yanzu abinda nakeso shine idan ka san akwai wani da kaga yanayi to kayi kokarin sanar dashi, muna fatan samun masu kananan sana'a ne maza da mata domin suci moriyar horon.


Sannan idan kana da wata shawara da kake ganin zaka iya bayarwa sai ka tuntubemu ta email info@sharfadi.com ko ta lambar waya 08035830253.


Basheer Sharfadi

CEO, Sharfadi Tech.

#OnlineBusiness

Almustapha suleiman kankia

abuabdullah.com.ng 

07035674655

No comments