[Fatawa] Shin zan iya dora riba akan abinda aka wakiltani insawo?

Share:

ZAN IYA DORA RIBA, IDAN AKA WAKILTA NI SAYO ABU 


Tambaya: Assalamu Alaikum Mallam, dan Allah ina da tmby, kaman misalin mutum yana baka kudi ka sayo mishi abu, wataran ya baka kudin ka sayo, wataran kuma sai ka sayo ka kai zai baka kudin, shin koya halasta inci riba a wanda yaban kudinshi in sayo mai, ko kuwa a wanda na sayo da kudina ne kawai zan iyacin riba, banda Wanda ya bada kudinshi? Nagode Allah ya kara basira.

Amsa: Wa alaikum assalam Allah ya amsa addu'arki 'yar'uwa, idan mutum ya wakilta ki, ya baki kudi ki sayo masa wani abu, bai halatta ki ci riba da shi ba, sai da izininsa, saboda hadisin Urwatu Al-ja'ady lokacin da Annabi s.a.w.  ya ba shi dinare (1) don ya sayo masa dabbar layya, sai ya sayo akuyoyi guda biyu, ya sayar da daya akan dinare daya, ya zo ma da Annabi s.a.w. da akuya daya da kuma dinaran da ya aike shi, sai Manzon Allah ya amshe ya yi masa addu'a, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 3642.

Kasancewar Annabi S.a.w. ya tabbatar da shi akan aikinsa, sai ya nuna hakan shi ne shari'a, don haka idan wakili ya samu ragi ko ya ci riba a cinikayyar da aka wakilta shi ya wajaba ya dawo da ita zuwa wanda ya aike shi.  

Idan ya wakilta bai bayar da kudi ba, to mutukar kuna kasuwanci a tsakaninku ya halatta a dora riba, amma in ba kwa yin kasuwanci ba za ki dora riba ba, za ki kawo masa abin a kudin da ake siyarwa a kasuwa, saidai in ya bada iznin cin riba, saboda wakili amintacce ne a shari'a, wasu malaman suna ganin za ki iya dora gwargwadon wahalarki, in bai bada kudi ba.


Allah ne mafi sani.


Don neman Karin bayani  duba Al-mugni na Ibnu khudaamah 5\86.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Almustapha Suleiman Idris Kankia

abuabdullah.com.ng 

07035674655

No comments