[[Fatawa]] Shin yahalatta mace tabi jam'in sallah daga gidanta?

Share:

               ﷽
TAMBAYA: MALAM SHIN YA HALATTA MACE TA RIKA BIN SALLAR JAM'IN MASALLACI, AMMA DAGA 'DAKINTA NA AURE?
(Daga Boddo Nafada)
AMSA: Saboda muhimmancin wannan tabayar taki, nayi nufin amsata tun ranar da kika rubuto ta.
Kuma nayi bincike mai zurfi akan mas'alar har na rubuta zan turo sai battery na ya mutu.
**amma ga summary na binciken da nayi:
# IMAMUSH SHAFI'IY yace bai halatta ba ta kowacce fuska.
# IMAMU MALIK yace ya halatta kubi kowacce sallah daga cikin gida amma banda Jumu'ah.
# IMAMU ABU HANIFA yace ya halatta kubi kowacce sallah.
Sai dai ina ganin zai fi agareku kubi shawarar da Manzon Allah (saww) ya gaya ma wata mata (UMMU HUMAYD). Yace mata:
"SALLAR ATSAKAR GIDANTA YAFI TAJE TAYI A MASALLACI, KUMA SALLARTA ACHAN CIKIN DAKINTA SHINE YAFI ALKHAIRI FIYE DA SALLARTA ATSAKAR GIDANTA"
(Abu Dawud ne ya ruwaitoshi)
Kubi maganar wannan hadisin shine zai fi agareku. domin kuwa bin sallah daga nesa yana da disadvantages da yawa, misali:
Idan aka samu matsalar daukewar wutar lantarki zaku iya rikicewa ku rasa yadda zakuyi ku Qarasa sallar.
Duk lokacin da aka samu matsalar sujjadah Qabali ko ba'adi, ba lallai ne ku ku fahimta ba.
Don haka yin taku daban ita ce mafi lada, mafi samun nutsuwa.
WALLAHU A'ALAM.

Almustapha Suleiman Idris Kankia
abuabdullah.com.ng
07035674655

No comments