[[ Fatawa]] Shin ya Halatta Abi mutun Fasiki Sallah

Share:
 

                     ﷽

HUKUNCIN BIN FASIQI SALLAH 

TAMBAYA: Assalamu Alaikum Sunana Sulaiman Abubakar Lambata. Allah Ya sakawa Malam da alkhairi Yakara Fahimta Inada Tambaya Malam Ya halatta Abi Liman Fasiki?. Ma'ana Matumin dake Rike 'Yan mata Da maganganun Batsa ?.

Allah Bada Ikon Amsawa Bissalam.

AMSA: Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Eh ya halatta abishi Sallah Mutukar dai yana da ilimin sanin hukunce-hukuncen Sallah din. Amma bisa Mazhabinmu na Malikiyyah yin hakan Makruhi ne. (akwai karhanci).

Amma abinda yafi kyau kuma yafi dacewa shine asamu wanda ya fishi salaha (kyawun halaye) da kiyaye dokokin Allah koda bai kaishi ilimi ba.

WALLAHU A'ALAM.

Almustapha suleiman Idris Kankia

abuabdullah.com.ng 

07035674655

No comments