[[Fatawa]] Hukuncin Zubda ciki a Musulunci

Share:


HUKUNCIN ZUBDA CIKI A MUSULUNCI :

TAMBAYA: Salamu alaikum Ina son Malam yai man bayani akan matsayin zubda ciki (abortion) a musulunci. Nagode daga Wata Dalibar Zauren Fiqhu.

AMSA: Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Zubda ciki koda na kwana daya ne, haramun ne a Musulunci. Ba ya halatta a zubar da ciki sai in akwai wani karbabben uzuri wanda shari'a ta yarda dashi.

Idan cikin yana matsayin makonnin farko ne, wato Qasa da watanni biyu, kuma akwai matsalar wata babbar jinya ko tsoron rasa ran Matar dake dauke dashi, to ya halatta azubar.

Idan kuma yakai matsayin Kwana tamanin zuwa 120, to haramun ne a zubar dashi koda akwai dalili. Sai dai in manyan likitoci masanan bangaren sun tabbatar da cewa idan aka barshi zai iya zama hanyar rasa ran Matar dake dauke dashi.

Idan kuma yakai Wata hudu zuwa sama, to ba ya halatta azubar dashi ta kowacce fuska sai dai in likitoci sun tabbatar da cewa in aka barshi zai kaiga rasa ran wacce ke dauke dashi. Kuma duk da haka ba za'a zubar dashi ba har sai likitoci sun bi dukkan hanyoyin da zasu iya bi don guje ma faruwar hakan.

Amma zubar da ciki don tsoron abin kunya, ko don tsaron talauci, ko tsoron wahalar kula da yaro, wannan duk haramun ne. Duk tabbas duk wanda ya aikata haka alhaki zai fara binsa dmtun anan duniya, kuma sai Allah ya tambayeshi akansa gobe Alqiyamah.

WALLAHU A'ALAM.

Almustapha suleiman kankia

abuabdullah.com.ng 

07035674655

1 comment: