[Fatawa] Dai daitawa Tsakanin yaran daka haifa

Share:

        ﷽

ADALCI TSAKANIN 'YA'YA

Kamar yadda Allah Ta'ala ya azurta da dama a cikinmu da 'ya'ya to mu sani fa ze tambayemu ranar gobe qiyama ko munyi adalci a tsakaninsu. Amana ce wacce iyaye yakamata su lura da ita sosai.

Ibn Qudamah a cikin al-Mughni (5/666) ya ce:

Malamai sunyi ittifaki cewa mustahabbi ne daidaita tsakanin 'ya'ya kuma makaruhi ne banbanta tsakaninsu.

Mazhabar Hanabilah ta ce haramun ne mahaifa su banbanta tsakanin yaransu wajen kyauta ko makamantansu (kashshaaf al-Qina'a, 4/310; al-insaaf, 7/138).

Haka suma 'yan Zahiriyyah fahimtarsu kenan.

Ibn Taimiyyah yace idan akwai dalilin da Shari'a zata iya amincewa dashi toh babu damuwa (Majmu'ul Fataawa, 31/295).

Akwai Hadisin da Bukhari (2586) da Muslim (1623) suka fitar na Baban Al-Nu'man bn Bashir, ya fadawa Manzon Allah (SAW) cewa ya baiwa danshi kyautan wani bawanshi se Annabi (SAW) ya tambayeshi, sauran yaran naka fa, su ma duk ka basu? Se yace a'a, sai Annabi (SAW) yace toh kyautar batayi ba, ka karbi bawanka.

A wata ruwayar ta Muslim ma, Annabi (SAW) yace masa: "Kada ka nemeni shaida akan abinda kayi domin ni bana bada shaida akan zalunci".

Nuna banbanci tsakanin 'ya'ya ze iya haifar da gaba da kiyayya tsakanin yaran da kuma rashin tausayin mahaifa.

Amma idan a cikin yaran akwai masu matsala ko larurar da suke bukatar kulawa na musamman toh hakkin iyayen ne suyiwa sauran yaran bayani don su fahimta. (Kitabul Adl bainal Aulad, shafi na 22). Wannan shine ra'ayin Shaikh Bn Baaz (Fatawaal Jami'ah lil Mar'atil Muslimah, 3/1115, 1116).

Allah muke roko ya bamu ikon yin adalci tsakanin 'ya'yanmu.

Almustapha Suleiman kankia
abuabdullah.com.ng 

No comments