﷽
Tambaya: Malan ance dole waliyin mace ya zama musulmi. To, idan na ga yarinya ina so, amman Ubanta kirista nest. Daidai ne ya aurar da ita gare ni?
Amsa: Ai inda aka ce waliyi ya zan musulmi, sai wadda za a aura-musilma ce, amman in kafura ce (Ahalul-kitab) tilas sai Ubanta mai addini irin nata ya daura mata auren.
Sai dai in ta zamo musulma. wannan kuma Ubanta, ba zai aurar da ita ba, sai a sami wani musulmi ya aurar da italia.
ALLAH Shine mafi sani
Sheik Abubakar Mahmud Gumi
fatawa mai lamba ta 115
Almustapha Suleiman Idris kankia
abuabdullah.com.ng
07035674655
No comments