Fatawa akan Tsarki

Share:

                     Fatawa akan Tsarki                           
                ﷽              
TAMBAYA: malan mutum ne yayi bawali (fitsari); sai bai sami ruwa ba ,haka nan bai sami dutse bay; sai ya karkabe.Da kuma lokacin sallah ya yiddish, sai ya tafi ya yai alwalla ya yi sallah. To , yaya sallarshi take?
AMSA: To, in dai ya karkabe, yana da alwallah. Cewa aka yi "kada ka yi sallah , kana dauke da kazanta". Watau dai , in ya sa hoge, ko ya sa dutse, ya goge, yaje ya yi alwallah ya yi sallah, ya halatta. Amman idan bai yi ba, har ya zan akwai kazanta nan gareshi, sannan ya yi alwalla; bai tuna ba sai bayan ya gama sallah; in akwai lokacin sake sallar nan (lokacin bai fita bay) to, sai ya sake. In kuwa babu lokaci, shi ke nan sallarsa ta yi. Domin kuma  akwai Ruwaya, ga khilafa gun Malik,cewar: shin gusar da kazanta, ga tufar maisallah,  ko jikinsas, ko wajen zamansa; wajibi nest, ko sunnah ne? in an ce wajibi ne, to ko lokaci ya wuce sai an sake. Amman in sunnah ne, to in lokaci ya wuce ba za a sake bay.
To, amman ko a inda Malik ya ce wajibi ne, ya sa sharudda biyu: in da yace mutum ya tuna, kuma yana da ikon gusarwa. To , anan idan bai tuna ba fan? ko bai da ikon gusarwa? To, ashe ke nan sai akwai lokaci, zai sake.
ALLAH ne mafi sani.

         Sheik Abubakar Mahmud Gumi
          fatawa mai lamba ta 1


Almstapha Suleman Idris Kankia
abuabdulla.com.ng
07035674655


No comments