Fatawa Akan Shafar gaban Namiji da Mace ko yana Karya Alwallah

Share:

                    ﷽

:

Idan Mutum ya shafa Azzakarinsa ko Mace ta shafa Farjinta, Shin hakan yana karya alwala kokuma a'a baya warwareta,

:

Amsa:

:

Alal-Haƙiƙa ansamu Saɓani tsakanin Malamai Fuƙaha'u dangane da wannan Mas'ala kan cewa shafar Azzakari ko Farji yana karya Alwala ko a'a? Ansamu maganganun Malamai dabam-dabam akan haka:

:

→(1)Ƙauli na farko shine, mafi yawan Malaman dake Mazhabobin MALIKIYYA, SHAFI'IYYA, HANABILA, suntafine akan cewa Shafar Azzakari ko Farji da nufin Sha'awa ko ba da nufin Sha'awaba da gangan yayi ko da kuskure, sukace alwalarsa ta karye, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da wannan Hadisi na

( ﺑﺴﺮﺓ ﺑﻨﺖ ﺻﻔﻮﺍﻥ )

Wanda Mαиzoи Aʟʟαн( ﷺ )* Yake cewa:

:

" ﻣﻦ ﻣﺲ ﺫﻛﺮﻩ ﻓﻠﻴﺘﻮﺿﺄ "

MA'ANA:

Wanda ya shafi azzakarinsa yasake alwala,

:

Sannan dakuma wannan Hadisi da Abu-Huraira ya ruwaito cewa Mαиzoи Aʟʟαн( ﷺ ) Yace:

:

" ﺇﺫﺍ ﺃﻓﻀﻰ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺑﻴﺪﻩ ﺇﻟﻰ ﺫﻛﺮﻩ ﻟﻴﺲ ﺩﻭﻧﻬﺎ ﺳﺘﺮ ﻓﻘﺪ ﻭﺟﺐ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﻮﺿﻮﺀ "

MA'ANA:

Idan ɗayanku ya shafi azzakarinsa da hannunsa batare da wata sutura atsakaniba Haƙiƙa alwala ta wajaba agareshi:

:

Danhaka sukace waɗannan Hadisai guda biyu dukansu Hujjane akan cewa shafar azzakari ko Farji yana karya alwala, domin tayiwu yasa sha'awar Mutum tamotsa har wani abu yafito ta gabansa batare da yasaniba danhaka akace yasake,

:

→(2)Ƙauli na biyu shine, Mazhabin HANAFIYYA suntafi akancewa Shafar azzakari ko farji da nufin Sha'awa ko ba da nufin Sha'awaba sukace baya karya alwala, wato Akasin Ƙauli na farko kenan, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da wannan Hadisi da akayiwa Mαиzoи Aʟʟαн( ﷺ ) tambaya cewa: idan Mutum yana cikin Sallah sai yashafi azzakarinsa Shin zai sake alwala? Sai Aηηαвι( ﷺ ) Yace:

:

" ﻻ، ﺇﻧﻤﺎ ﻫﻮ ﺑﻀﻌﺔ ﻣﻨﻚ "

MA'ANA:

A'a (bazai sakeba) domin (shima azzakarin) gaɓace daga jikinka,

:

Danhaka kenan anan Aηηαвι( ﷺ ) Yace azzakari gaɓace kamar sauran gaɓoɓi, ta yadda idan Mutum yashafi wata gaɓa ajikinsa kamar hannu ko ƙafa baza'ace sai yasake alwalaba, to hakanan shima azzakari, sannan sukace wadancan Hadisai guda biyu nafarko dasuke nuna cewa alwala tana karyewa idan anshafi gaba, sukace dukkansu basu ingantaba, danhaka a Asali alwala bata warwarewa harsai in ansamu tabbas, kamar yadda Aηηαвι( ﷺ ) Yake cewa:

:

" ﻻ ﻳﻨﺼﺮﻑ ﺣﺘﻰ ﻳﺴﻤﻊ ﺻﻮﺗﺎ ﺃﻭ ﻳﺠﺪ ﺭﻳﺤﺎ "

MA'ANA:

Kada (maiyin sallah) yajuya yafita daga sallarsa harsai in yaji ƙaran tusar dayayi kokuma yaji warinta, wato yasamu tabbas kenan cewa tawarware,

:

→(3)Ƙauli na uku shine, wasu Malaman suntafine akan cewa idan Mutum yashafi gabansa da nufin Sha'awa don yaji daɗi to alwalarsa ta karye, amma idan yayi shafarne ba danufin jindaɗi ba to alwalarsa tananan, wato su waɗannan Malamai sunaso suhaɗa dukkan Hadisan suyi aiki dasune, kamar yadda yake sanannen abu awajen Malaman Usul shine, sukance

( ﺍﻟﺠﻤﻊ ﺃﻭﻟﻰ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﺮﺟﻴﺢ )

MA'ANA:

In zeyiwu ahaɗa Hadisan da sukaci karo dajuna ayi aiki da kowanne hakan shi yafi dacewa akan arinjayar da ɗaya daga cikinsu,

:

Kenan Hadisin da yace alwala ta warware ana nufin idan Mutum yayi Shafa danufin jindaɗi, amma Hadisin da yace bata warwareba ana nufin idan yayi Shafa ba danufin jindaɗi ba, kamar idan yana wankan tsarki sai yashafi gabansa ba da niyyaba, ko kamar idan yana sosa jikinsa sai yashafi gabansa, kokuma wani abu makamancin haka,

:

→(4)Ƙauli na huɗu kuma shine, maganar Malaman da sukatafi akan cewa Shafar azzakari ko farji da nufin Sha'awa ko ba da nufin Sha'awaba baya karya alwala, danhaka sukace wancan Hadisin da yace asake alwala ma'anarsa itace Mustahabbine ga wanda yashafi gabansa yasake alwala, amma ba dole bane, daga cikin Malaman da sukatafi akan wannan ra'ayi akwai

Shaikhul-Islam-Ibn-Taimiyya, kuma da yawa daga cikin Malamai suna rinjayar da wannan Ƙauli naƙarshe:

:

※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※

:

ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυ ננ α мαι ƙαяғι:

:

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:

↓↓↓

:

" ﺍﻟْﺈﻧﺼﺎﻑ " ‏( 1/202 ‏)

:

" ﺍﻟﺸﺮﺡ ﺍﻟﻤﻤﺘﻊ " ‏( 1/234 ‏)

:

" ﺍﻟﻤﺠﻤﻮﻉ ﻟﻠﻨﻮﻭﻱ '' ‏( 2/42 )"

:

" ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ ﻹﺑﻦ ﻗﺪﺍﻣﺔ " ‏( 1/119 ‏

Almustapha Suleiman Idris Kankia

abuabdullah.com.ng 

07035674655

No comments