Fatawa akan Sallar WALHA

Share:
                      Fatawa akan Sallar WALHA

                                              ﷽


BAYANIN SALLAR WALLAHA A TAƘAICE
Sallar Wallah tana cikin sallolin nafila mafi falala wadda Manzon Allah ﷺ yayi a aikace kuma ya KWADAITAR akanyinta,sunnace mai karfi daga cikin sunnonin
Manzon Allah ﷺ da yake kiyayeta hatta a lokacin
Bulaguro
HUKUNCIN SALLAR WALLAHA_*
Sallar Wallaha sunnace mai karfi wadda aka
kwadaitar akan kowane musulmi ya raya wannan
Sallar domin dacewa da abu biyu koyi da Manzon
Allah ﷺ da bin Umarninsa da kuma dacewa da falala da lada mai yawa.
● ﺑﻦ ﺑﺎﺯ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :-
Yana cewa:-Sallar Wallah sunnace ta Manzon Allah s.a.w mai karfi wadda ya aikata ta kuma ya kwadaitar DA Sahabbansa akan aikita ta.
Allah yana cewa:{ ﻭَﺍﻟﻀُّﺤَﻰ } ‏[ ﺍﻟﺾﺣﻰ 1 :]Allah yana rantsuwa da Hantsi ko wallaha idan
Allah yayi rantsuwa da wani abu to yana nuna
girmama wannan abu da matsayinsa awajan Allah".DAGA CIKIN FALALAR SALLAR WALLAHA
Hadisan Manzon Allah ﷺ masu yawa sunzo masu bayyana falalar sallar wallaha,ga kadan daga cikinsu;-
1-Yazo acikin Hadisil Qudsy,Allah mai girma da Buwaya yana cewa:-{Dan Adam,kayi min Raka'o'i guda hudu a farkon yini,zai isarmaka wannan yinin zuwa karshensa}
@ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 475 ).
Wannan yana bayyana mana dukkan wanda yayi
sallar Wallaha raka'a hudu a farkon yini to Allah zai isar masa zuwa karshen yinin da kariyarsa da taimakonsa na musamman.
ﺍﻟﻄﻴﺒﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ :
Yana cewa;
An zan isar maka al'amuranta da shagulgulanka da
baka kariya da kiyayeka daga abin ki bayan sallarka ta wallaha har zuwa karshen yini,......"*.
@ ﺗﺤﻔﺔ ﺍﻷﺣﻮﺫﻱ : 2/478 .
2-Manzon Allah ﷺ yana cewa;
(Jikin mutum akwai gabobi guda 360,kuma an dora masa yin sadaka akan kowace gaba)* sai Sahabbai suka ce masa:
"Wa zai iya sauka wannan nauyi ya Manzon
Allah ??" sai yace;
(Goge majinar ko kakin da akayi a masallaci,ko
dauke wani abin cutarwa daga akan hanya,idan
kuma mutum bai sami damaba,to yayi sallah raka'a guda biyu na Wallaha ya isar masa)*
@ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ , ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ .
3-Manzon Allah ﷺ yana cewa;(Babu mai kiyaye Sallar wallaha sai bayin Sallah
masu yawan komawa zuwa ga Allah,sallar wallaha sallace ta bayanin Allah masu yawan konawa zuwa
ga Allah)
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ .ADADIN RAKA'O'IN SALLAR WALLAHA_*
Mafi karancin Sallar wallaha raka'a biyu,amma bata
da adadi wajan yawanta ko nawa ka iyaye,amma
wasu Malaman sun tafi akan mafi yawanta shine
raka'a Takwas kamar yanda Manzon Allah ﷺ bai wuce raka'a takwas ba kamar yanda Hadisin Ummu hany R.A ta ruwaito.LOKACIN SALLAR WALLAHA.
Lokacin Sallar wallaha yana farawane daga fitowar rana ta dan daga kadan kamar bayan fitowar rana da minti 30 zuwa 45am har zuwa gab da zawalin rana daga tsakiya da yan mintina biyar.
@ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( 14/ 306 )).
Wato kamar;
Daga karfe 7am zuwa 11:45am.
MAFI FALALAR LOKACIN SALLAR WALLAHA.
mafi falala da alkhairin lokacin yin Sallar
Wallaha,shine lokacin da rana ta fara zafi
sosai,lokacin da mutane sukafi shagaltuwa da
aiyukansu na yau da kullum,kai kuma sai ka shagaltu da gani da Ubangijinka,gab da zawalin rana.
@ ﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ ‏( 6/148 ).
ﺑﻦ ﺑﺎﺯ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :-
Yana cewa;Abinda yafi muhimmanci shine idan mutum yana da damar yinta a lokacin mafi falala to yayi amma
idan baya da dama to yayita a farkon yininsa,amma yinta lokacin da rana tafara zafi sosai yafi.
ZIKIRIN DA AKE KARANTAWA BAYAN SALLAR WALLAHA_*
Daga Nana A'isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tace;Manzon Allah ﷺ yayi Sallar wallaha,sannan yace; ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ , ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ , ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ.
ALLAHUMMAGH FIR LI,WA TUB ALAIYA,INNAKA
ANTAT TAUWABUR RAHEEM.
har sai da ya fadi hakan sau 100.
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺍﻷﺩﺏ ﺍﻟﻤﻔﺮﺩ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 619 .
● ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
Yana cewa:Sallar wallaha idan lokacinta ya wuce to ta wuce ba'a ramawa domin Sallah ce mai lokaci
kayyadadde.
● ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:Sallatul Ishraki wato Sallar hantsi itace sallar
wallaha afarkon lokacinta,kuma sunnace ta kowace rana.
Allah ne mafi sani
Allah ka bamu ikon kiyaye wannan sunnah mai girma amin.

No comments