SIFFAR YADDA AKE RAMUKON SALLAH :
TAMBAYA: Assalam da fatan malam na lafiya, ya ibada
da hakuri da jama'a?
Ina da wasu tambayoyi da nake so ataimaka
min da amsoshinsu.
1] Nine na makara sallar asubah, ban tashi
daga barci ba har sai 7 oclock (karfe
bakwai) rana ya
fito kuma naji ance alokacin ne shaidan
yake matso da kahonsa kusa da rana, idan
mutum na sallah alokacin tamkar shi
shaidan din yake bautawa.
To awani lokaci ne ya kamata mutum ya
rama wannan sallan?
[2] Akwai salloli da ake bina bashi na
shekaru 2 Wanda nake so
in fara biya. misali idan alokacin sallar
magrib ne bayan na idar sai
kuma nake so in biya azahar na bashin da
ake bina yaya zan biya tunda
sallar zuhr a asirce ne kuma ana lokacin
magrib na bayyanawa ne.shin zanyi sallar a
asirce ne ko yaya.
Thanks daga Sani Jauro.
AMSA: Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
Da farko dai waccen labarin da ka fada, ba
haka yake kai tsaye ba. Amma dai abinda ya
tabbata a hadisan Annabi (saww) shine :
Imamu Ahmad da Muslim sun ruwaito hadisi
ta hanyar Sayyiduna Amru bn 'Abisah
(radhiyallahu anhu) yace "Nace wa Manzon
Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam)
"Ya Annabin Allah bani labari game da
sallah".
Sai yace "Ka sallaci sallar asubah sannan ka
kame daga yin sallah har sai rana ta fito, ta
'dago domin ita tana fitowa ne ta tsakanin
Qahon wani shaidani kuma awannan lokacin
ne kafirai suke yi mata Sujadah ...".
Imamun Nawawiy yace "Shi shaidanin yana
kusantar da kansa ne zuwa ga rana a irin
wadannan lokutan domin ya zamanto masu
yi mata sujadah daga cikin kafirai tamkar shi
suke yiwa sujadar a zahiri".
To kaga anan Manzon Allah (saww) ya
bayyana cewa an hana yin sallah ne a irin
wadannan lokutan saboda kada muyi
tarayya da kafirai cikin irin abinda suke yi
adaidai lokacin. To amma wannan hanin bai
shafi sallolin ramuko ba.
Mafiya yawan Maluman Fiqhu sun tafi akan
halaccin yin ramuko (Qadha'i) koda bayan
sallar asubah ne ko bayan la'asar Sun
dogara da Ingantaccen hadisin da Bukhariy
da Muslim suka ruwaito Manzon Allah
(saww) yace "DUK WANDA YA MANTA DA
WATA SALLAH, TO YA SALLACETA IDAN YA
TUNOTA".
Don haka ita sallar ramuko babu wani
lokacin da aka hana yinta. Zaka iya yinta
akowanne lokaci. Kuma zaka yita ne bisa
yanayin da ta tsere maka, kuma akan
yanayin da ake yinta.
Misali idan sallar azahar ce ko La'asar zaka
yi karatunsu a boye ne koda acikin dare
zaka ramasu. Sannan koda sallar asubah
zaka rama, ko maghriba ko isha'i to zakayi
karatunsu afili ne koda da rana zaka
ramasu.
Hakanan sallar da ta tsere maka alokacin
kana gida, zaka yita ne cikakkiya (ba Qasaru
ba) koda sanda zaka ramasu din kana wajen
tafiya ne. Haka kuma sallolin da suka tsere
maka akan yanayin tafiya ko balaguro, to
zaka ramasu ne bisa yanayin sallolin tafiya
(Qasaru) koda kuwa agida zaka ramasu).
Don Qarin bayani ka duba babin dake
bayanin yadda ake ramukon sallah acikin
littafin Risalatul Qairawaniy, Muqaddamatul
Iziyyah, da Matnul Ashmawiyyah, da Matnul
Akhdhariy.
Anan nake so inyi maka gargadi game da
barin sallah ta wuceka da gangan, ko kuma
yin sakaci wajen ramasu. Wannan haramun
ne domin kuwa yana daga cikin wasa da
sallah. Kuma Allah yace "AZABA TA
TABBATA GA MASALLATA. MASU YIN
SAKACI AKAN SALLARSU".
Kaji tsoron Allah ka kiyaye dokokinsa. Sallah
ita ce mafi girman dukkan ibadodi kuma ita
za'a fara dubawa a ikin ayyukanka aranar
Alkiyamah. Idan tayi kyau ka tsira. Idan
kuma ta 'baci (saboda rashin yinta akan
lokaci, ko rashin yinta da ilimi, ko rashin
sanya tsoron Allah cikinta) to mutum yayi
asara mai girma. (Allah shi kiyayemu).
WALLAHU A'ALAM.
Almustapha suleiman Idris kankia
abuabdullahi.com.ng
07035674655
No comments