Fatawa akan mata masu Istima'i

Share:

                 ﷽

TA KAMU DA MATSALAR ISTIMNA'I :

TAMBAYA : Assalam malam da fatan kuna lafiya ya kokari da jama'a Allah ya saka muku da alheri.

Nayi aure shekaru 3 kenan tun kafin nayi aure nake fama da jarabawa na isti'ma'i har ynzu nakasa rabuwa da shi nasan kuma haramun ne abinda yafi damuna shine bansan ta yadda na iya wannan abin ba kawai tsintar kaina nayi a ciki kuma dana gama sai in tsinci kaina cikin nadama da kunyar ubangiji na narasa yadda zan rabu da wannan abu kuma ina fama da matsalar namijin dare A dalilin haka nayi bari sau uku ynzu inada ciki haihuwa ko yau ko gobe.

Amma nakasa rabo da wannan abu kuma ynzu bana mafarki da namijin daren sedai inyi mafarki mata na biya wa junan su bukata to idan ba na dage ba ina farkawa senayi don Allah ataimake ni da addu'a har ruqya an taba yi min amma ba abinda naji.

AMSA: Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Istimna'i haramun ne bisa ittifakin Maluman Mazhabin Malikiyyah da kuma mafiya rinjayen Malaman Musulunci, bisa dogaronsu da ayoyin cikin suratul mumineena da suratul ma'arij wajen da Allah yake bayanin siffofin bayinsa Muminai, yace :

"KUMA SUNE WADANDA SUKE KIYAYEWA GA FARJOJINSU, SAI DAI BISA MATAIKUNSU DA KUMA ABINDA HANNAYEN DAMANSU SUKA MALLAKA (WATO KUYANGINSU).

"DUK WANDA YA NEMI ABINDA KE BAYAN WANNAN, TO SUNE MASU QETARE IYAKA".

Da kuma ayar suratun nur inda Allah Subhanahu wa ta'ala yake cewa :

"KA GAYA WA MUMINAI MATA SU RUNTSE IDANUWANSU KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU, WANNAN SHI YAFI TSARKAKEWA GARESU... ".

Kuma tabbas bincike ya tabbatar da cewa istimna'i yana haddasa illoli ga zuciya da dabi'a da lafiyar jikin Dan Adam. Kuma yakan janyo ma masu yinsa matsaloli masu yawa. Tun daga ciwukan jiki da kwakwalwa, har zuwa kan shafar aljanu.

Koda yake bisa fahimtar da nayi wa bayananki, naga alamar tabbas akwai shafar Aljanu tare dake Kuma su suke haifar miki da mafarke-mafarken, tare da ingiza zuciyarki zuwa ga sa'ba wa mahaliccinki.

Amma duk da haka ya zama wajibi kiji tsoron Allah Subhanahu wa Ta'ala, ki rika kallon kusancinsa gareki, kuma cewa Shi mai shaida ne bisa ayyukan bayinsa. Yana kallonki duk lokacin da kika buya domin yin wannan mummunan abun. Kuma ki rika tuna ranar gamuwarki dashi.

Cewa anyi miki ruqyah sau daya ba'a kama aljanun ba, ba hujjah ce dake nuna cewa basa jikinki ba. Domin akwai mutanen da akan shafe sama da shekara guda ana yi musu ruqyah kafin a samu nasarar kamawa ko Qona shaidanun dake tare dasu.

Don haka kije kici gaba da neman magani tare da bin irun shawarwarin da muke bayarwa anan Zauren Fiqhu kamar :

- Yawaita karatun Alqur'ani da salati da zikirin Allah ko yaushe. Musamman lokutan barci da kuma safiya da maraice.

- Ki nemi Man Habbah ki tofa fatiha, ayatul kursiyyi, suratul feel, Li'eelafi, Qul Huwallahu, falaqi da nasi kamar Qafa 3-3. Ki rika shan cokali guda safe da yamma, kina shafe jikinki dashi.

Ki samo Muhrikul Jinni kina shafawa domin Qonesu koda basu bayyana ba. Sannan ki rika shan Na'a-Na'a domin samar da lafiya ga jaririn dake cikinki.

Allah ya sawwake, ya shiryeki ya baki lafiya damu baki daya, ameen.

       Almustapha Suleiman Idris kankia

         abuabdullah.com.ng

         07035674655

No comments