Fatawa akan mace mai Haila ta Taba Alqur'ani

Share:

                  ﷽


HUKUNCIN YIN KARATUN ALQUR'ANI GA MAI HAILA :

Tamby: mal. Idan mace bata da tsarki bazata karanta Alqur'ani ba, ko ta ta'bashi.To ko a waya ne bazata iya karantawa ba ko ta tabawa? tunda shima Alqur'ani ne .

AMSA: Wa alaikumus salam.

Bisa Mazhabinmu na Malikiyyah mace mai haila ba zata dauki takardun Alqur'ani ba. Amma ya halatta gareta tayi tilawar abinda ta riga ta haddace.

Kuma ya halatta ta karanta ayoyi biyu ko uku domin ta'aweezi (neman tsari). Hakanan kuma zata iya karanta Application na Alqur'ani irin wanda ke cikin Manhajar Wayoyin Android..

Kuma kamar yadda kika ji acikin audio na karatunmu na littafin Ahalari, akwai hadisai ingantattu da dama wadanda suka zo da maganar haramcin ta'ba Alqur'ani ga Mace mai haila. Duk da cewa wasu Maluman sun raunana wasu hadisan daga ciki, to amma komai raunin hadisi yana sama da duk wani ijtihadin da Malamai zasuyi akan mas'alah. Kuma dukkan Maluman hadisi sun yarda da cewa ana aiki da rarraunan hadisi akan abinda ya shafi gargadi ko kwadaitarwa.

WALLAHU A'ALAM.

Almustapha Suleiman Idris Kankia

abuabdullah.com.ng 

07035674655

No comments