Fatawa akan JINI

Share:


                  ﷽

JINI YANA ZUWA MIN A YAYYANKE!

TAMBAYA:Assalamu Alaikum, malam matata ta haihu sati biyu kenan, to malam yanzu takan wuni jini bai zo ba, sai da daddare in ta kwanta sai jinin ya zo, to shin malam za ta iya yin wanka da safe tayi sallolin azahar zuwa isha'i? Ko kuma yaya za ta yi? Nagode Allah ya kara ilimi mai albarka.

AMSA:To dan'uwa a zance mafi inganci duk yinin da ta ga jini to yana daukar hukuncin jinin biki ne, haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk yinin da ba ta ga jini ba, sai dai idan yana yayyankewa kusa-kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba ta ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: "bai sanya muku kunci a cikin addini ba" suratul Hajj: To dan'uwa a zance mafi inganci duk yinin da ta ga jini to yana daukar hukuncin jinin biki ne, haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk yinin da ba ta ga jini ba, sai dai idan yana yayyankewa kusa-kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba ta ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: "bai sanya muku kunci a cikin addini ba" suratul Hajj: 78.

Allah ne mafi sani.

Don neman karin bayani duba Almugni na Ibn Khudaamah 1/214.

Almustapha suleiman Idris kankia

abuabdullahi.com.ng 

07035674655

No comments