Fatawa akan haihuwa da sa suna ga jariri

Share:

                  ﷽

TAMBAYA: Malan wai ko ana hada hudubar jariri da sanya masa suna ne a lokaci daya?

AMSA: Ba'a ce ana fadar sunan yaro a lokacin huduba ba. Cewa aka yi a rana ta ukku (bayan haihuwa), mahaifin yaron zai yi kiran sallah ga kunnen dama, sannan zai yi ikama ga kunnen hagu. Sannan kuma sunan da za'a ambata na yaro, idan kana da ragon da zaka yanka, to sai ka bari sai a rana ta bakwai, ranar da zaka yanka ragonka sai ka ambaci sunan yaron. Idan kuwa baka da ragon, to duk lokacin da kake so, sai kasa masa sunan, ba saian kai kwana Bakwai ba. kuma idan rana ta Bakwai din tazo, kana iya fadin sunan yaron kamin ka yanka Ragon, ko bayan yankan Ragon, duk daya ne, amman dai ba'a yankan ragon sai rana ta fito.

Sai dai ina kara yi muku gargadi gameda ragon nan, domin mutune na matsawa kansu akan dole sai sun yanka ragon, su sawa kansu wahala kawai.

Ko jiya na ba wani misali, da ya tambayeni cewar bai da ragon, gashi an haifar masa 'ya'ya biyu. Don haka yace yana son yasan yadda zai yi, wato ko zai iya jinkirtawa ( yankan ragonan)? Sai na ce masa:"ka san in zaka yi Ruku'i cikin sallah, zaka ce "ALLAHU AKBAR!" to, wanna kabbarar da zaka yi, tafi ragon sunan nan mustahabbi nest. Don haka maganar jinkirtawa ai bai ma ko taso ba, domin ko mutum na da halin yankawar, sai bai yi ba, ba'a cewar yayi haram balle ace ana binshi bashin hakan."

Sheik Abubakar Mahmud Gumi

Fatawa mai lamba ta 410

Almustapaha Suleiman Idris

abuabdullah.com.ng

07035674655

No comments