Fatawa akan Auren wadanda ba musulmai ba

Share:

AURAN KAFURAI KAFIN SUN MUSULUNTA INGANTACCE NE!!

Tambaya

Assalamu alaykum, don Allah ina son a tambaya min malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya musulunta shi da iyalan sa ta dalili na, kuma ni na basu kalmar shahada. Su na da yara manya da kanana, sai suka tambaye ni ya ya matsayin auren su nace auren su na nan kamar yadda shariar musuluncinta tsara, sai yace min to yaya matsayin yayan su? To gaskiya wannan ne ban sani ba shine nake son a mika min wannan tambaya ga malaman Allah yataimaka ameen

Amsa

Wa alaikum assalam, To ɗan'uwa auran da kafurai suka yi kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi akan ƙa'idoji da sharuɗan da suka yarda da su na auratayyarsu, saboda Annabi S. A. W bai canza auran kafiran da suka musulunta ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda da 'ya'yayansu da suka haifa ta hanyar wancan aure. Sahabban Annabi S. A. W. da yawa an haife su ne ta hanyar auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da dangantakarsu zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan da kafurai suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi zuwa iyayansa bayan sun musulunta.

In kafirai suka yi zina suka haifi Ɗa ba za'a danganta shi zuwa baban sa ba bayan ya musulunta.

Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma sharhul Mumti'i 12/239.

Dr Jamilu Zarewa

13-09-1438

08-06-2017

Almustapha suleiman Idris

abuabdullah.com.ng 

07035674655

No comments