Fatawa Akan Aure

Share:
                                                              Fatawa akan aure
                                                                          ﷽


TAMBAYA: Malan mutun ne yake neman auren wata yarinya wadda har anyimata Baiko dawani, sai yaba iyayenta kudi suka fasa dawancan sai suka aura ma wanda yabasu kudi. To malan miye hukuncin yin hakan?


AMSA: To babu wannan auren nashi, sai dai in an mayar mashi da kayan shi kuma ya karba (Mai Baiko), shi kuma ya amsa ya nuna yarda da warwarewar BAIKONSA, wato kenan ya yarda ya saki. Domin yin BAIKON nan kulla aure ne, don haka ba za'a sake daura wani aure a kanshi ba, har sai in ya yarda ya saki, wato in ya amshi kayansa da aka mayar mashing. To anan in aka daura auren ga na biyu shikenan auren yayi. Amman in ba haka bay, wato in bai saki bay, in aka daura wani auren babu shi.
Wato ga yadda abin yake: ko daga kai sai yaro, kace na baka diyata ka aura, shi kuma yace ya karba, shikenan aure ya tabbata, kai kuma uban yarinya baka iya koma aurar da ita ga wani.
Wato, cewar da kayi ka bashi diyarka aure yasa ta zan matarshi, abinda kawai za'a yi ba shine ba'a iya kaita gidan miji (wato tarewa) har sai shaidu sun tabbatar da an bashi auren, sannan an yanka mishi sadaki, (shikuma sadikin ya biya ko ya kaddara ga ranar da zai biya, wato bashi).
To, in an koma kuma ga wanda ya iske an yiwa wani mutum BAIKO da wata, sai ya nemi ya karkatar da wannan don ya komo ga kanshi to wannan Haramun ne ya aikata; domin karkatar da matar mutum zuwa gareka, ko ga wani daban, Haramun ne.
Ammandai matukar an ba na farkon abinda ya bada, ya yarda ya saki ,to in an daura auren da kai (na biyun) auren yayi, wancan auren kuma laifi na Haramun yana nan daban. Amman duk da haka idan shari'a ta gane wancan shirin tana iya hana yin wancan auren na biyu. Hakanan ma ,ko idan mijin farkon ya kai kara, anan ma shari'a na iya hanawa ayi wannan auren, ko da kuwa mijin farkon ya yarda ya saki.
Wato,bari in kara bayan anan, gameda cewar BAIKO ma aure ne: Wato,shari'a tace, rukunin aure hudu ne, da sharadi guda hudu. Rukuni farko shine a san mijin a san matar, (wato a san masu auren, na cewar dan wane zai auri wance diyar wane).
Sannan rukuni na biyu, shine a sami waliyyin mata wanda zai ce ya aurar da da ita (shine ubanta, ko dan uwanta ko dai wani mutum). Sannan rukuni na uku shine Siga,wato maganar da za'a daura aure da ita , (ace na aurar maka da ita shi kuma yace ya aura), shikenan SIGA  ta tabbata. Sannan rukuni na hudu , shine a sami SHAIDU da zasu yi shaida akan wannan.
To,wadannan sune rukunnai Hudu idan aka hadasu aure ya tabbata.
To sai kuma sadaki, wanda yake shi sharadi ne ba cikin rukunnai yake bay, domin yana yuwuwa ya taketa (saboda rukunan) ba'a cewar yayi zina , sai dai a yanka masa sadkin ya biya, ko da daga baya ne.
To, wajen BAIKO  kuwa ai duk sai an tabbatar da rukunan nan sadaki ne  kawai ba'a ambata,ko amsa. Saboda haka ne Malamai ke cewar NIKAHUN TAFWULU ne.
A takaice dai yin BAIKO ma daura aure ne, don haka in anyi BAIKO ba'a daurawa wani aure kuma, sai in wanda aka yiwa BAIKON ya saki.
ALLAH shine mafi sani.
Fatawa mai lamba 437 ta
Sheik Abubakar Mahmud Gumi


          Almustapha saleiman Idris kankia
          abuabdullah.com.nguni
            07035674655

No comments