Fatawa akan aikin Hajji

Share:

                  Fatawa akan aikin Hajji                          
                             ﷽
ZAN IYA YIWA MAMACI AIKIN HAJJI?
Tambaya
Assalamu alaikum wa rahmatullah, Malam Barka da dare
Malam ina tambaya ne dangane da wakilci a aikin hajji (Anniyaabatu anil mayyit), mahaifina yana son yiwa wani daga cikin makusantan shi da ya rasu; sai wani mutum (malami) yake ce masa ai akwai addu'ar da ake yi (qul huwal laahu sau wani adadi da dai sauransu) wadda tafi wannan aikin hajjin da za ai masa!!
To dan Allah Malam yana so ne yaji shin hakan ya tabbata, kuma dai-dai ne? , ko akwai wani Malami da ya fadi hakan?
Ka huta lafiya!
Amsa:
Wa'alaikum assalam, Ba haka ba ne, wannan maganar ba ta da asali, Yiwa wani hajji ya tabbata a hadisai, wani mutum ya tambayi Annabi (S.A.W) cewa: "Babana ya mutu bai yi hajj ba, zan iya yi masa?, sai Annabi (S.A.W) ya ce yaya kake gani Idan da bashi ya bari za ka biya masa? sai yace E, sai Annabi (S.A.W) yace to ai bashin Allah shi ya fi cancanta a biya, don haka ka yi masa hajji, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya rawaito a Muntaka a hadisi mai lamba ta: 1797, da kuma Darakudni.
Sannan Kathamiyya ta tambayi a Annabi (S.A.W) cewa: Hajji ya riski babanta yana tsoho za ta iya yi masa? sai Ya ce E, kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta; 1756.
Malaman fiqhu sun kafa hujja da wadannan hadisan tabbatattu akan halacci ko wajabcin yiwa mamaci ko wanda ba zai iya ba aikin hajji Idan yana da hali.
Hajji ibada ce mai zaman kanta,kuma daya daga cikin ginshikan musulunci babu yadda za'a yi wata addu'a ta zauna a makwafinta.
Allah ne mafi sani.
12/7/1437
20/4/2016
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Almustapha Suleiman Idrs Kankia
abuabdullah.com.ng
07035674655

No comments