Murnar sabuwar shekara

Share:

*MURNAR SABUWAR SHEKARA KOYI NE DA KIRISTOCI*:
Daga *Abdurrahman Abubakar Sada*
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: "Sai kun bi hanyoyin wadanda suka gabace ku taka-bayan-taka, zira'i-da-zira'i (duk abin da suka yi sai kun yi), da ace dayan su (Banu Isra'ila), wani ya shiga ramen damo, lallai sai kun bi su ga shiga ramen (cikin al'ummata sai an samu mai shiga ramen), kamar yadda cikin wadancan magabata suka shiga, sai wani ya tambaye shi ya ce; ya Rasulallah! Al-Yahudu Wan-Nasara, sai ya ce; eh".
Yanzu ga shi nan ana aiko ma mutane sakon Barka da Sabuwar Shekara.
Don Allah zamanin Manzon Allah an yi sabuwar shekara ko ba a yi ba?.
Annabi ya taba yiwa wani barka da sabuwar shekara?.
Don me za ka yi?.
Ina aka samo barka da sabuwar shekara (murnar sabuwar shekara)?.
Kiristoci (su ke Happy New Year). Shi ya sa su sabuwar shekararsu ko aiki ba su yi.
To shi ne su kuma 'Yan Darika suka tura Gwamnati, su ma sai aka yi declearing din sabuwar shekarar Musulunci (Work Free Day), wannan nasaranci ne.
Idan ba mu yi hattara ba, baki ne Manzon Allah (S.A.W) ya yi mana, shi ne zai hawanmu!.
Baki ne Annabi ya yi mana cewa; duk abinda Yahudu da Nasara suka yi, cikin al'ummarsa sai an samu masu yi.
To shi ne; Yahudu da Nasara sun yi Happy New Year ko ba su yi ba?.
To shi ne sai aka samu wasu wawaye! Wai Barka da shiga sabuwar shekara! Ina barka take?.
A baya kadan muna cikin shekara ta 2018, yanzu kuma mun shigo cikin shekara ta 2019.
Cigaba muka yi ko kamawa baya muka yi?.
Domin adadin kwanakin da aka lizimta maka sun kara ragewa.
Don Allah murna ya kamata ayi maka ko jaje?.
Amma saboda Yahudanci da Nasaranci dake cikin zukatan wasu, ba jaje suke yi ba, murna suke yi.
Idan mutum ya ce maka; "happy new year", ka ce masa; "I'm Not a Cristian" (ni ba kirista ba ne), kiristoci su ke happy new year.
Don haka murnar shiga sabuwar shekara, da bukukuwan da wasu kungiyoyi na Bidi'a masu amsa sunan Musulunci suke shiryawa, duk koyi ne da kiristoci.
Misali: Maulidi, duk duniya! Duk wanda ya ce maka ya fi Sayyidina Abubakar, ko Umar, ko Usman, ko Ali, ko Aisha, ko Hafsah, ko duk Sahabban nan (Radhiyallahu Anhuma) son Manzon Allah (S.A.W), kai ka san wannan makaryaci ne.
Wai shi yanzu zamansa nan wai ya fi su son Manzon Allah.
Don haka saboda son da yake yiwa Manzon Allah (wanda ya wuce na Sahaba), ya fito da wani abu don Murnar Zagayowar Ranar da aka haifi Manzon Allah (saboda so).
Wanda dukkanin Sahabban Manzon Allah babu wanda ya taba yi, kai ka san wannan tataccen makaryaci ne.
Don haka babu Sahabi guda cikin Sahabban Manzon Allah (wanda ya taba yin Maulidin zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah).
Amma ga Maulidi nan al'ummar Manzon Allah suna yi.
Ina suka samo shi?
Kiristoci suna yin Bikin Kirsimati (ranar da aka haifi Annabi Isah (A.S).
Sannan wadanda ba Annabi ba kuma yanzu birthday.
Yanzu da yawan mutane, duk shekara sai sun yi yekuwar murnar zagayowar ranar haihuwarsu.
Tabbas bakin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ne ke biye da al'ummarsa, ya ce; "LA TATTABI'UNNA SUNANA MAN KANA KABLAKUM".
'Yan uwa a yada mana wannan fadakarwa, domin kaucewa tarkon yahudawa da nasara.
Allah ka tsare mana imaninmu.

No comments