Fatawar malamai

Share:
FATAWA AKAN MAFARKIN MUMINI
                              ﷽
TAMBAYA: Mene ne gaskiyar cewar da ake yi wail, mafrkin mumini , wanibangarene na annabta?
AMSA:"RU'UYA MUMINUN JUZ'IN MIN SITTATIN WA ARBA'INA JUZ'IN MINAN-NUBUWWA", wato, shine: 'Mafarkin salihi (na kwarai), juz'i ne daga Arba'in da shida na Annabci'.
Domin kamar yadda malamai suka fassara, lokacinda wahayi ya fara zuwa ga Annabi ﷺ , ya fara zuwa masa da mafarki ne, a cikin wta shidda na farkon (Annabcin),a lokacin nan in yaga mafarki, sai ya bayyana gaskiya nest.
Bayan hakanan, yayi shekara ashirin da ukku wahayi na zuwa gareshi. To, shine malamai suka yi fassarar cewar: Idan aka dauki wta shidda nan, zai kama ga kowace shekara akwai wata shidda-shidda sau biyu. To, shekara ishirin da ukku nan, idan an kasa susan, kashi biyu-biyu, ya zamo Arba'in da shidda kenan, wato, shine aka ce: wanda yayi mafarki na kwarai, yayi kenan bangare daga Arba'in da shidda din nannies. Wato kamar ya shiga bangaren nan na farko kenan.
To, wannan kuma, bai nunawar mutum ya zama Annabi kenan, domin cikin mafarki, akwai wanda ke gaskiya, akwai wanda ba gaskiya bane. Don haka ,in kayi mafarkinka, sai ka daidaita shi da Alqur'ani ko Hadisi, ka gani, in kaga yayi daidai, to , wannan babu laifi kayi aiki da shi, ba akan an baka sabon abu bay, sai dai akan musulunci ya taho dashing.
Saboda haka , ba'a iya yin hujja da wannan, ace wani na iya samun wani sabon hukunci ta hanyar mafarki.
ALLAH SHINE MAFI SANI
Fatawr sheik Abubakar Mahmud Gumi
mai lamba ta 206
Almustapha Suleman Idris kankia
abuabdullah.com.nguni
0735674655

No comments