Fatawar malamai

Share:
Fatawar Sheikh  ABUBAKAR GUMI
Akan mijin daya ba matarsa takardar saki amman bata buda ta karantaba balletasan menene a ciki sai ya karba ya yaga minene hukuncin yin hakan?
                                               ﷽
AMSA: To, rubutu ya kasu kahi buyu ne, to idan mutum yayi nufin saki, "yasaki wance", ya rubuta ya kawo ya ajiye cikin daki, yana shirin  bata , to ko bata gani bay, saki ya auku, tunda yayi niyya, kuma ya rubuta hakan.
To, amman in yana shakka (shawara) na cewar: Ko ya saki wance? ko kada ya saketa?, sai yace to bari dai ya rubuta ya ajiye, idan hankali ya nutsu akan ya saketa, shikenan ya bata takardar. Idan kuma yayi nazarin kada ya saketa, sai ya yaga.
To, sai yayi hakan , wato , ya rubuta ya ajiye, amman bai sakin bay, yana jiran ya tabbatar,  ko kada ya tabbatar. To, ita wannan takardar daya rubuta, idan matar bata gani bay, wani ma bai gani bay,to yana iya yaga abinsa; idanya yanke shawarar kada yayi sakin. Idan kuwa ta riga ta gani, ko wani ya gani, to shikenan saki ya tabbata(ko da yayi shawarar kada ya saketa).
sabda haka , aure babu wasa a cikinsa, kamar kuma yadda babu aure ma babu wasa a cikinsa, domin ko da wasa mutum yace ma wani "Na baka diyata, wance aure" shi kuma wanda aka ba ya karba , shikenan aure ya tabbata , sai in ya saki.
Hakanan ma wajen 'yantawar wuya shima babu wasa a ciki, domin ko da wasa kace ka  'yanta bawanka, to shikenan ya 'yantu.
ALLAH shine mafi sani.
 fatawa mai lamba 451

           Almustapha suleiman Idris
           abuabdullah.com.nguni
           07935674655

No comments