Fatawa akan sayarda takin Masai

Share:

HUKUNCIN SIYAR DA TAKIN MASAI
                                  ﷽
TAMBAYA :Akramakallahu, menene hukuncin saye ko sayar da taki na masai? (kashin mutane wanda aka fito da shi daga shadda) don yin amfani da shi a gona?


AMSA:To malamai suna kasa wannan gida biyu :
1. dan ya zama ya canza daga najasar zuwa wani suna daban, to wannan ya halatta a siyar da shi a zance mafi inganci, kamar takin zamani, bincike ya nuna ana hada shi da kashin mutum lokacin da ake yinsa, saidai tun da siffarsa ta canza daga siffar kashin mutum din ta hanyar magungunan da aka sanya masa, ka ga zai zama ya halatta a siyar da shi.
2. Wanda yake yana nan a sifarsa ta kashin dan'adam, to wannan mafiya yawan malamai suna hana siyar da shi saboda najasa ne, saidai malaman Hanafiyya suna halattawa, idan ya cakudu da kasa mai yawa, saboda bukatuwar mutane i zuwa hakan. Duba Raddul-muktar 5\57 Shafi'iyya kuma suna halatta amfani da shi amma suna hana siyar da shi, duba raudhatu dalibina na Nawawy 3\352
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
17/7/2014

No comments