Yadda zaka duba sakamakon jarabawar WAEC

Share:

Da farko zaka ziyarci shafin yanar gizo-gizo wanda ake duba sakamakon a can mai adireshi kamar haka :

https://www.waecdirect.org

Sai ka sanya lambar jarrabawa WAEC dinka a gida na farko. (lambobi guda 7 na cibiyar (centre) din da kayi Jarrabawar sai kuma lambobi guda 3 na Jarrabawar ka ma’ana lambobi guda 10 zaka shigar.Sai ka zabi shekarar da kayi Jarrabawar a gida na biyu.Sai ka zabi irin Jarrabawar da kayi ma’ana Private ce ko kuma irin tamu? (School Candidate Results)Sai ka sanya Serial Number din dake jikin katin Jarrabawar ka.Sannan ka sanya PIN din dake jikin katin Jarrabawar ka.Sai ka danna “Submit” ka jira ya danyi loading kadan zai nuno maka sakamakon ka.

Allah Ya Baiwa ‘Yan Uwa Dalibai Sa’a Amin.

No comments