Yadda a kasami ma'aikatan bogi budu hamsin a Nigeria

Share:

Basheer Journalist Sharfadi
Yadda Aka Bankado Ghost Workers Dubu Hamsin A Nigeria
Menene Ghost Workers?
Sune ma'aikacin da yake karbar albashi sama da guda daya, a
shekarun baya a Nigeria misali mutum yana aiki a hukumar
zabe to sai yaje wata hukumar ya nemi aiki kuma a bashi,
baya zuwa amma ana biyansa wannan albashin sai ka samu
mutum daya da albashin mutum uku, ya toshe gurinsu.
Idan albashinka na ma'aikatar farko da kake kake aiki ya fito
daga TSA Asusun Bai Daya na Gwamnatin Tarayya zuwa
bankin ka sai Remita tayi copy din BVN dinka ta turawa
gwamantin tarayya haka in na wata ma'aikatar yazo sai remita
ta turawa gwamantin tarayya cewa wane-wane ma'aikaci a
hukuma kaza ya karbi albashi sau kaza.
Da aka tsananta bincike sai da aka gano mutane Dubu
Hamsin (50,000) masu irin wannan halaryar cikin ma'aikatan
gwamnatin tarayya.
Sai aka dakatar duk wanda aka samu da wannan laifin ya
zama albashi daya zai dinga karba, hakan yasa gwamantin
tarayya ta samu rara har sama da Naira Biliyan Dari Biyu
N200,000,000,000.
Acikin wannan kudinne kwanaki gwamnatin tarayya ta debi
'yan sanda Dubu Goma (10,000) ake biyansu albashi, ba wai
wasu kudin albashinsu ne gwamnatin ta sake fitarwa ba.
To wannan shine yadda aka bankado Ghost Workers.
Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
December, 2018.

No comments