Wayyo cikina

Share:

Wani Bakatsine da wani Banupe ne su ka yi laifi, sai a ka
kai su kotu. Ga yadda zaman kotun ya kasance.
Alkali :- Sakamakon ina cikin farin ciki da haihuwar mata
ta lafiya, zan yi mu ku rangwame. Kowa ya fadi
iyakance yawan bulalan da ya ke so a yi ma shi, da kuma
yadda ya ke so ayi masa bulalan.
Banupe :- Toh, ranka ya dade, ina so a yi min bulala goma,
amma a dora filo guda goma ajiki na, kafin a
fara bulalan!
Alkali :- Babu laifi, ku yi masa yanda ya ce. Aka yi wa
Banupe bulala 10, ba tare da ya ji zafi ba.
Alkali :- Bakatsine?.
Bakatsine:- Ranka ya dade, ina son a yi min bulala (100),
amma a dora wannan Banupen a baya na, kafin
a fara bulalan!
Alkali :- Babu laifi. Ku dora shi a bayan sa, a yi masa
bulalan!! A ka yiwa Banupe bulala (100) a matsayin
Bakatsine…!

No comments