Musha dariya😁😁😁😁😁

Share:

Wani saurayi ne yaje wajen budurwar sa hira suna cikin
hirar sai NEPA suka kawo wuta sai ya tambaye ta yace
yanaga ko, ina da wuta amma banda gidan ku?
Sai tace wlh lokacin ana ruwan sama shine iska ta tsinke
WAYAR. Sai yace to meyasa baku kira YAN NEPA sun
gyara ba?
Sai tace, wallahi mun kira su sunce zasu zo gashi yau
har kwana biyu shuru. Sai yace bakomai, abinda za,ayi
shiga gida kisa YARA SU FITOMIN DA TSANI DA KUMA
FILAYA.
Sai tace haba kawai ka barshi za,a gyara, SWEET HEART
kaga ba aikin ka bane. sai yace haba MY LOVELY ai abun
duk bigene.
Aka fitomai da TSANI DA SAURAN KAYAN AIKI ya hau
FALWAYA ya fara aiki. Can zuwa wani dan lokaci sai
budurwar sa taji yayi wani MUGUN IHU HADE DA KARA
wuta ta jaho sa kasa ya fado cikin KWATA A SUME.
Bayan ya farfado daga suman da yayi, ya tashi zaune
yana daga kansa sai yaga budurwar sa da baban ta da
babarta da yaran gidan gaba daya da kuma sauran yaran
unguwar suna mai sannu.
Can saiji yayi wata karamar yarinya kanwar budurwar sa
tace, LA! AUNTY SAURAYIN KI YAYI KASHI A WANDO.

No comments