Ma'anar asusun TSA

Share:

Me Ake Nufi Da TSA (Asusun Bai Daya)?

Menene TSA (Treasury Single Account)?
A da can kowacce ma'aikata dake karkashin gwamnatin tarayya tana da account dinta a bankin da taga dama kuma zata iya yin sama da account guda daya da zata dinga ajiye kudadenta, tana sarrafasu yadda yakamata idan shekara tayi sai ta tattara dukkan bayanan abinda tayi (Annual report) cewa tayi kaza, da kaza ga kuma abinda ta kashe ga ragowar kudin, ko kuma a'a kudin bai isheta ba ma, wannan rahoton yana iya zama gaskiya ko karya, don haka duk abinda hukuma ta rubuta ta Kaiwa accountant general haka zai karba ba zai gane ba.

Nigeria tana da ma'aikatu kusan guda dubu daya 1,000 banda kuma ma'aikatun da suke karkashin jihohi suma suke yin hakan.

Tsohuwar Ministar kudi Ngozi Uwela da tsohon gwamnan babban bankin Nigeria Mai Martaba Sarkin Kano na yanzu Malam Muhammadu Sanusi II sai suka kawo tsarin BVN (Bank Verification Number) da TSA (Treasury Single Account) wato asusun bai daya a hausance, karkashin wannan tsarin zai zama asusun gwamnatin tarayya yana babban bankin kasa na CBN to dole duk hukumomin nan su rufe account dinsu da suke dashi a baya, ya zama idan za'a turawa wata ma'aikata kudi to kai tsaye za'a tura zuwa ga account guda daya na gwamnatin tarayya.

Sai dai a lokacin gwamnatin wancan lokacin bata aiwatar da tsarin ba saboda wanda zasu aiwatar sune suke satar kudin.

A baya idan baku manta ba idan dalibi zai biya kudin makaranta zai biya ne ta account din makaranta amma yanzu ba haka abin yake ba, kai tsaye dalibi zai biya zuwa ga account din gwamnatin tarayya, kuma babban bankin kasa CBN da accountant general suna ganin duk zirga-zirgar da kudi keyi daga ko ina ta wannan account din.

Wannan shine TSA Asusun Bai Daya.

To yanzu gwamnati tayi account dinta a CBN kuma ba irin sauran bankuna ba GT, First Bank, UBA, d.s, to shin ta yaya za'a tura musu kudi?

Shine sai ake amfani da tsarin remita.

Menene Remita?
Remita: shine zai hadaka da account din gwamnatin tarayya wato (TSA) ba'a tura kudi ace wai baiyi ba, remita akwai kyaky-kyawan tsari na zirga-zirgar kudi.

Idan ka biya kudi ta remita kai tsaye zai tafi account din gwamantin tarayya sannan ta nan ne gwamnatin tarayya take biyan albashi da kuma alawee na 'yan bautar kasa.

Idan gwamati ta bayar da umarnin a biya albashin ma'aikata to remita zata tsara sannan ta turawa bankin ma'aikaci, shi kuma banki umarni ne aka bashi don haka dole ya tura maka cikin account dinka, CBN da accountant general yana kallo.

Remita: Kamfanine mai zaman kansa ya fara aiki a shekarar 2005, remita yana da Iznin shiga bayanan kowane banki a Nigeria domin ya aika da kudi.

Zamu dakata anan sai a rubutu na gaba.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
December, 2018.

No comments