Karanta yadda zaka sami followers a istagram dinka

Share:


[Ka Karanta Yanzu] Hanyoyi Goma (10) Da Zaka Samu Followers A Instagram

Ana Yi Muna Jin Dadi InstagramSocial Networks

 December 19, 2018Basheer Journalist SharfadiLeave A CommentOn [Ka Karanta Yanzu] Hanyoyi Goma (10) Da Zaka Samu Followers A Instagram

NASIBI PAINTER Muna Yin Aikin Fentin Gidaje, Screeding, P.O.P Sutuko & Wolfefa Domin Karin bayani sai a kiramu ta lambar waya kamar haka: 08067501339

Hanyoyi Goma (10) Da Zaka Samu Followers A Instagram

Wadannan jerin hanyoyine har guda goma mai amfani da dandalin Instagram zai bi domin samun yawan followers.

Rubutuka Masu Alaka:

Instagram Zai Bada Damar Dora Video Mai Tsawon Sama Da Awa Daya

Yadda Tsarin Kasuwancin Instagram Yake

1. Ka hada Instagram dinka da sauran Social Media platforms, ana hada instagram da facebook, twitter, flickr d.s, hakan zai baka dama duk sanda kayi posting kai tsaye zai tafi sauran shafukan da ka hada.

2. Ka sanya alamar instagram a facebook page dinka, yana da muhimmanci a shafinka na facebook ko profile ka saka instagram dinka hakan zai taimaka maka wajen kara samun followers a insta.

3. Ka dinga amfani da HashTag mai alaka da abinda kayi posting kuma mai yawan jama’a, misali nayi posting akan shan miyagun kwayoyi to zanyi ta #DrugAbuse zanga mutane nawa suka biyo wannan HashTag dina a Insta, ko #Kano d.s.

4. Ka dinga tagging din abokananka, yin tagging a instagram shima hanya ce da yake kawo yawan followers.

5. Ka dinga following din mutane sanna ka dinga yiwa mutane liking.

6. Ka dinga yin posting masu kyau wanda zasu ja hankalin mutane.

7. Ka dinga tsara lokutan yin post ba kara zube ba, lokutan da aka fi son kayi post a instagram shine karfe 05:00pm da kuma karfe 08:00pm.

8. Amfani da Sticker a story: Yanzu a story na Instagram zaka iya sanya sticker kala-kala wadda zata ja hankalin jama’a, hakan yana taimakawa wajen tara followers.

9. Tambaya a Live Video: amfani da tambaya a live video yana taimakawa sosai wajen karin samun followers domin zai baka dama ka sanya wata tambaya wadda zata ja hankalin jama’ar ka.

10. Ka Biya Instagram kudi suyi maka promotion su kara maka yawan followers.

Allah ya bada sa’a.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
18-12-2018.

No comments