Hukumar jarabawar shiga jami'a (JAMB)

Share:

Yadda Hukumar Jamb Ta Lakume Ma'udan Kudade Ba Tare Da Hakki Ba

A can bayan hukumar shirya Jarrabawar share fagen shiga jami'a ta Jamb itace ke yin uwa makarbiya wajen harkar kudin yin register Jamb din.

Kuma tun da aka fara Jamb har zuwa shekarar 2015 abinda Jamb ta baiwa Gwamnatin tarayya matsayin haraji shine kusan Naira Miliyan 56, N56,000,000 a lokacin duk shekara abinda take baiwar gwamnati bai wuce Miliyan Uku ba N3,000,000.

Lokacin da aka fara biya ta remita sai Ministan kudi ta wancan lokacin Kemi Adeosun tace sai sun biya Miliyan Dari Biyu N200,000,000 sabanin Miliyan Uku da suke biya a baya, sai jamb tayi magana da Minista din, sai tace ta rage musu su tabbatar sun kawo Miliyan Dari N100,000,000.

Abin mamaki a wannan shekarar an sakawa jamb ido ana ganin duk abinda take, sai gashi Jamb ta kawo Naira Biliyan Takwas N8,000,000,000 a shekara daya kawai! 

Wannan ne ya sanya majalisar tarayya ta fara binciken shin ina sauran kudaden na shekarun baya suka makale?

Shine akace wai Miciji ya hadiye Miliyan Talatin Da Shida N36,000,000.

Wani abu sai Nigeria!  Kudin da baima kamata ace an ajiye tsurarsu a office ba, amma wai har an ajiyesu miciji ya cinye.

Mai karatu a wannan shekarar ta 2018 mai karewa Jamb ta kawo Naira Biliyan Tara N9,000,000,000!.

Har yau a matsayina na Dan Nigeria ina fatan naga an cigaba da wancan binciken ko saboda na gaba sa hankalta.

Allah ya kyauta.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
December, 2018.

No comments