HATTARA YAN ACHABA: Ankama matar da ke ma yan achaba kwachen mashin

Share:

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta bayyana nasarar
cafke wata mata mai suna Zinatu Abubakar, mai shekara
19 da haihuwa a duniya, da ta kware wajen yi wa yan
kabokabo satar baburansu a cikin garin Katsina.
A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan-
sandan jihar ya fitar S. P. Gambo Isa, ya ce matar ta
kware sosai wajen yi wa masu haya da babura kwace a
cikin garin Katsina.
Ya kara da cewa asirinta ya tonu ne a lokacin da Gide
Wada, ya dakko ta daga Kofar-Kaura zuwa unguwar
Sokoto Rima Quarters cikin garin Katsina.
SP Gambo Isa ya kara da ce Wada ya fadi kasa warwar
bayan ya ci wani abin tsotso da matar ta bashi sanda
suna cikin tafiya.
Daga nan ne fa sauran yan kabokabo suka bi matar suka
damko ta suka hannanta ta ga jami’an Yan-sandan inda
take ta maida yadda take yi wajen satar baburan .
Daga karshe kuma ya kira yi masu san’ar kabokabon da
su daina amsar duk wani abin ci ko sha a hannun
wadanda suka dakko su

No comments