Hanyar samun managarciyar Haddar Alqur'ani mai girma

Share:

HANYOYIN SAMUN MANAGARCIYAR HADDAR AL-QURANI MAI GIRMA

Sheik Àliyu Said Gamawa (Hafizahullah).
1. Ka fara haddar ka da addu’ar neman taimakon Allah cikin wannan niyya taka ta alheri.
2 Ka kula sosai da kanka wajen nisantar kazamtar haramun, wato ka tsaya wajen cin halal, domin cin
haram yana toshe basirar Dan Adam.
3. Ka nisanci fara hadda don burin samun dukiya, kuma ka cire kwadayin abin duniya a zuciyarka. Haddar Alqur’ani bata zama a cikin kwakwalwar duk wanda ya
matsu yaga ya tara dukiya a cikin haddar sa da zafi-zafi.
4. Kayi karatu a wajen Malami na Allah wanda yasan Karatun, Kuma serious malami wanda ya maida hankalinsa akan hidimtawa Alkur’anin.
5. Ka nemi goyon bayan mahaifan ka tare da rokon addu’arsu, don sanya albarka daga iyayenka ginshiki ne wajen nasarar samun haddar ka cikin sauki.
6. Kaifin basira da hazaqa yana taimakawa wajen saurin samun yin hadda mai kwari cikin karamin lokaci.
7. Ka fara hadda da niyya mai kyau, wato ka zamo mai kwadayin son karatun da burin haddar alkur’ani.
8. Ka zamo mai juriya akan kowacce irin wahalar da zaka riska a wajen neman karatun ka, ka cire son hutu da yawan kasala ko son nishadi da wargi da zai jawo maka lalaci.
9. Tanadin abinci yana da muhimmanci don ka samu natsuwa, don ba’a iya hadda mai kyau da yunwa amma kar kace sai kaci mai kyau kasha mai kyau a kullum.
10. Kar ka sanya gaggawa wai sai ka gama hadda a karamin lokaci, ka natsu ka bi a hankali domin
ba’a samun ilimi a cikin dare daya.
11. Samun abokan karatu na kirki da zaku na tafiya tare cikin hadda yana taimakawa, amma ka kiyaye Idan fa abokanka suka zamo na banza, ko wadanda basa son karatun ko masu kasala to tabbas ka hadu da matsala da ci baya a harkar karatun ka.
12. Ka tsara gwargwadon abinda zaka na haddacewa a kullum, wato kamar ka tsara cewa a duk cikin kwana 3 zaka yi haddar allonka ko shafi daya ko biyu ko makamancin haka..
13. Ka rika karanta wuraren da ka haddace a cikin Sallar ka ta farilla da nafiloli a kowanne wuni.
14. Idan da dama ka nemi allo ka rubuta da kanka wajen da kake son ka haddace, ko ka samu littafi mai rubutun da idon ka zai karanata sosai, sannan kayi ta QwamI.. Ba-ji ba-gani.
15. Ka tsarawa kanka lokaci a cikin safiya da maraice kana tilawa na maimaita wurin karatun ka adadi mai yawa, wato kana biyawa a kullum kamar sau 100 in zaka iya.
16. Ka za6i yin tilawa da dare da jijjifin safiya, ka tsara yadda zaka Qaranta barcinka, kuma abinda yafi shine kana bacci da wuri don ka samu tashi cikin dare, ka kula wajen cin abinci madaidaici, Ka takaita yawo da surutu maras amfani da zaman wurin hira. kuma ka rage yawan abokai.
17. Ka kula sosai da yawan ibada da nisantar aiyukan sa6o.
18. Ka gujewa sauraron wakokin banza da
raye-raye da kallon film don suna makantar da zuciya.
19. Ka tsare harshen ka daga batsa da zagin mutane da kallon haramun da latse-latsen waya maras amfani.
20. In kana samun wahalar rike hadda kayi hakuri ka dogara ga Allah, ka yi juriya ka nisanci debe tsammani da karaya a zuciyar ka. Lallai in kana himma da dagewa zaka samu taimakon Allah.
Ina rokon Allah ya karfafa niyyar mu, ya cika mana burin mu ya hore mana saukin hadda ya bamu karatu mai albarka. Amin yarabbil alamin.

1 comment: