HAJJIN BANA GWAMNATIN JAHAR KATSINA TAFITAR DA KUDIN AJIYA

Share:

Hajjin bana: Gwamnatin jihar Katsina ta kayyade Naira
300,000 a matsayin kudin ajiya
Maigirma gwamnan jihar katsina Rt Hon Aminu Bello
Masari Dallatun katsina matawallen Hausa ya Amince da
Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar katsina da ta fara
karbar kudin Ajiya ga masu niyyar zuwa aikin Hajjin dubu
biyu da sha Tara (2019 Hajj) tun daga naira Dubu Dari
ukku zuwa abinda ya wuce haka daga wannan watan
Nuwamba (2018) har zuwa Maris na sabuwar shekara
(2019) kamar yanda Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa
(NAHCON) ta umarci jihohi.
Ana Bukatar kowane maniyyacin aikin Hajjin na 2019 Hajj
da su ziyarci ofisoshin Hukumar dake shiyyoyinta kamar
haka Daura, Katsina, Kankia, Dutsin-ma da kuma
Malumfashi domin bude Asusun Ajiyarsu tare da fara
biyan kudin kujerar su tundaga wannan watan da Muke
ciki.
Saboda haka Hukumar na shaida masu cewa ana bukatar
maniyyaci daya ziyarci ofisoshinta na shiyyar da ya fito
da Takardar shaida ta banki watau bank drapt,Hotuna
guda sha biyu,Takardar shaida ta karamar
Hukumar,Takardar shaida ta muharrami da kuma Wanda
zaya tsaya ma maniyyaci watau grantor.
Daga karshe Hukumar na gargadi ga kowane maniyyaci
ya tabbatar ya biya kudin shi ta hangar Takardar ta shaida
biya ta banking ba tsabar kudi ake karba ba,kuma suyi
Hulda kai tsaye da jami’anta dake ofisoshinta na shiyya
guda bakwai dake fadin jahar nan.
Allah ya bada ikon yin hakan ameen sanarwa daga
Badaru Bello Karofi Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar
jin dadin Alhazai ta jihad Katsina.

No comments