Gamnan katsina Aminu masari yakai ziyara ga yan gudun hirar zamfara agarin Faskari

Share:

Daga, Ibrahim M Bawa
A yanzun gwamman jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Masari
Masari ya ziyarci sansanin yan gudun hijirar al’ummar
jihar Zamfara da suka gudu zuwa karamar hukumar
Faskari domin tsira da rayukansu bisa iftila’in kashe-
kashen da suke fama da shi a jihar su.
Tun a jiya Talata 25 ga watan Disamba ne yan gudun
hijirar suka fara sauka a garin Yankara, inda daga bisani
aka wuce da su babbar Furamare dake tsakiyar cikin
garin Faskari
Masari ya jajanta wa mutanen sannan da iftila’in ya sama
sannan yi masu alkawarin cewa gwamnatin jihar Katsina
za ta basu kulawa ta musamman, sannan ya roki
al’ummar garin Faskari da duk wanda zai iya bayar da
gudunmuwarsa ga yan gudun hijirar kofa a bude take,
domin ceto su daga halin da suke ciki a yanzun
musamman na rashin muhallansu.
Sannan ya yi wa yan gudun hijirar albishir da cewa a ko a
yau din nan sai da mai girma shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya tura ministan cikin gida Janaral
Abdulrahaman Dambazau zuwa cikin Gusau babban
birnin jihar ta Zamfarar domin jajantawa al’ummar jihar
tare da tabbatar masu da cewa gwamnatin tarayya za ta
yi iya kokarinta wajen kawo karshen yan ta’adda da suka
dade suna yi wa mutane kisan gilla a nihar
Ya kara da cewa “A yanzun nan bayan mun kammala
wannan ziyar ta duba yan gudun hijirar mutane Zamfara
sama da dubu biyu a Faskari, daga nan kuma za mu
wuce Kankara domin duba inda can ma sama da yan
gudun hijira dubu biyu yan kauyukan jihar Zamfara ke
zaune a can” Inji Masari.
Shi ma a nashi jawabin shugaban riko na karamar
hukumar Faskari Alh Musa Ado ya ce sun karbi bakuncin
yan gudun hijirar sama da mutum dubu biyu maza da
mata, kuma karamar hukumar Faskari na kan aikin
taimaka masu da abinci da ruwa da wurin kwanciya da
magunguna ba dare ba rana.
Daga cikin wadanda suka tarbi gwamnan akwai shugaban
riko na karamar hukumar Faskari Alh Musa Ado, da
mataimakin Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina
kuma dan majalissar dake wakiltar karamar hukumar
Faskari Hon. Shehu Dalhatu Tafoki, hakiman Faskari da
na Mairuwa, da babban mai ba Gwamna shawara a kan
fannin ilimi mai zurfi Alh Bishir Usman Ruwangodiya da
sauransu.
Haka kuma akwai shugaban jam’iyyar APC na karamar
hukumar Faskari, da shugaban kungiyar Masari
Restoration Awareness Forum ta karamar hukumar
FaskariAlh. Ibrahim Garba Faskari da sauran manyan
dattawan jamiyyar daga ciki akwai Alh. Ibrahim Bala da
Alh Ahmad Musa Wapa Yankara, da Alh. Mu’azu Yahaya
Othman, da sauransu da dama.

No comments