FALALAR HADDAR ALQUR'ANI MAI GIRMA

Share:


FALALAR HADDACE QURANI:
Ya kamata mu sani cewa kafin mutum ya fara hadda ya duba yaga don Allah zai yi haddar.idan ya kyautata niyyarsa zai samu abubuwa dayawa a nan duniya da kuma lahira abubuwan da zai samu sun kunshi:
(1) ceto na alqurani ranar qiyama
(2) daukaka a cikin gidan aljanna
(3) za'a daraja shi a nan duniya mutane zasu ringa ganin kimarsa
(4) kwakwalwarsa zata bude
(5) ganinsa zai qaru sakamakon kallon shafin alqurani
(6) za'a saka shi a aljanna matukar yana aiki da abinda ya karanta
(7) za'a bashi ceto na dangin sa da sauransu.
(8) zai tara lada masu yawa domin duk harafi daya daya karanta lada goma..
Wadannan kadan daga cikin fa'idojin da mutum zai samu idan ya haddace qur'ani kenan.Mu dage da hardar alqur'ani mai girma..Allah yasa mu dace.

No comments