Abubakar Yahaya kusada ya amsa rantsu a zauren majalisar wakilai

Share:

Daga, Ibrahim M Bawa
A yau Laraba Kakakin majalissar wakilan tarayya Abuja
Hon. Yakubu Dogara ya rantsar da sabbin yan majalissar
wakilai guda uku da suka lashe zaben cike gurbi na yan
majalissun dokokin tarayya da ya wakana a jihohi uku.
Tsohon Kakakin majalissar dokokin jihar Katsina Rt. Hon
Abubakar Yahya Kusada daga jihar Katsina, dake wakiltar
kananan hukumomin Kankia, da Ingawa da kuma Kusada
na cikin wadanda suka yi rantsuwar kama aiki a
majalissar wakilan.
A kwai kuma na jihar Kwara da Bauchi dukkan su da suka
lashe zaben cike gurbin a karkashin tutar jam’iyyar APC.
A kawun majalissar ne ya gabatar da sabbin zababbun
yan majalissar, sannan Kakakin majalissar Dogara ya
basu rantsuwa.
Bayan kammala rantsuwar ke da wuya suka yi
musabahah da Kakakin majalissar da kuma shugaban
masu rinjaye Mr Femi Gbajabiamila, da sauran
takwarorinsu yan majalissar.

No comments